6 Disamba 2025 - 22:27
Source: ABNA24
Talauci Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Gabar Tekun Siriya

Yayin da talaucin da ba a taɓa gani ba ya mamaye gabar tekun Siriya, dubban iyalai an tilasta masu sayar da kayayyakin gidajensu, gonakinsu, har ma da abubuwan tarihinsu da aka bar masu domin su rayu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: "Waleed," wani mutum mai shekaru arba'in a wani ƙauye da ke gefen Tartus, yana tsaye a gefen hanya, yana son sayar da dutsen gugansa da tebur na katako. Yana yin hakan ne da fatan ceton ƙaramin ɓangare na hauhawar farashin rayuwa, bayan ya zama mara aikin yi da rashin matsuguni kuma an tilasta masa yin aiki a gonakin noma na yankin. Waleed, wanda a da memba ne na rundunar sojojin Siriya, ya taƙaita wahalar da tsoffin abokan aikinsa suke sha.

Ya shaida wa jaridar Al-Akhbar ta Lebanon cewa: "Tsawon watanni yanzu, ban sami damar samun aiki mai dorewa don tallafa wa iyalina ba. Aiki kusan babu shi a ƙauyukan Sahel, kuma yanzu galibi muna rayuwa ne bisa tallafin al'umma ko kuma ɗan kankanin kuɗin shiga na ma'aikatan noma hakan ma a yankin da ba isa muyi kuskuren barinsa ba, domin ana iya kama mu a kowane lokaci. Ako wane lokaci ana tilasta mini sayar da wasu kayan gida na don biyan buƙatun 'ya'yana na yau da kullun".

Yanayin Walid yayi kama da na dubban iyalai a yankin Sahel na Siriya, inda talauci ya kai wani matsayi da ba a taɓa gani ba kuma gwamnatin Jaulani ta yanke albashin sojoji da yawa da suka yi ritaya, musamman waɗanda aka warware matsalolinsu amma ba su da katin shaida; mutanen da ba su ma da damar ƙaura da neman aiki saboda ba su da katin.

Daga cikin waɗannan mutanen akwai "Hazar", tsohuwar ma'aikaciyar wani asibitin soja da aka rufe bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad da kuma korar ma'aikatanta. Ita da majinta sun daɗe suna kula da kansu, amma bayan shekara guda da aka shafe ana takun saka a siyasance da matakan tsuke bakin aljihu da suka shafi yaran Sahel, lamarinsu ya tabarbare.

"Basussuka sun taru kamar dutse a kanmu, kuma ni da mijina ba mu sami aikin da ya dace ba," in ji Hezar. "Dole ne mu sayar da wani ɓangare na gidan da muke zaune a ciki. Iyalina ba za su iya taimakawa ba; 'yan'uwana uku suna cikin soja, mahaifina kuma soja ne mai ritaya. Masu ba da gudummawa ba su gaza ba, musamman wajen samar da kuɗin burodi, amma abin da muke buƙata shi ne aiki mai kyau wanda zai biya buƙatun iyalin mafi ƙaranci".

Ba tare da samun damar aiki a Sahel ba, an tilasta wa wasu su gudu zuwa Lebanon ba bisa ƙa'ida ba don neman abin rayuwa da kuma guje wa barazanar tsaro. Amma waɗanda suka tsaya a baya an killace su a yankinsu, suna jiran buɗewa.

Abu Nasim, mai shekaru 70, uba mai 'ya'ya maza huɗu da 'ya'ya mata biyar, ya yi magana game da wahala biyu: Ina da gonar kaji don kiwon kaji da samar da ƙwai, kuma rayuwa ba ta yi muni ba. Amma bayan faɗuwar gwamnatin Assad, rayuwarmu ta rikide ta zama mafarki mai ban tsoro. Duk 'ya'yana maza suna cikin tsohuwar rundunar sojojin Siriya kuma yanzu suna zaune a gidana tare da iyalansu. Da rikicin tattalin arziki da shigowar ƙwai da kaji na Turkiyya, na yi asara kuma basussukana sun ƙaru. Na rufe gonar kaji, na sayar da babbar motata, na buɗe shagon sayar da kaji da ƙwai da ake shigo da su daga ƙasashen waje tare da 'ya'yana maza.

Ya ƙara da cewa: Ina ƙoƙarin kada in koma gida da wuri, domin ganin fuskokin jikokina waɗanda makomarsu ba ta da tabbas cikin karayar zuciya.

Sakamakon matsin tattalin arziki, mutane da yawa an tilasta maau sayar da kayansu na kansu, daga kayan daki da kayan lantarki zuwa wayoyin tarho, fitilun wuta, littattafai har ma da tsofaffin gilashi. Maher, mamallakin wani gungun gidaje, ya ce akwai ɗaruruwan tayi na filayen noma da gidaje a farashin da ya yi ƙasa da ƙimarsu ta gaske. Wasu suna sayarwa don shirya tafiya da ƙaura saboda ba su da fatan inganta yanayinsu. Wasu kuma ana tilasta musu sayarwa kawai don biyan buƙatunsu da biyan basussukan da suka tara tun bayan faɗuwar gwamnatin Assad.

Wasim, wani mai sayar da kayayyaki na second hand, ya yi bayani kan yanayin tafiyar kasuwancinsa: "Mutane suna cikin mawuyacin hali kuma suna sayar da duk abin da za su iya don samun kuɗi, ko da kuwa kaɗan ne. Wani lokaci ina siyan abubuwan da ba na buƙata kwata-kwata, kawai don kada in ɓata wa mai shi rai".

Tsarin tattalin arzikin yankin Sahel na Siriya, wanda ya dogara sosai kan noma, ya sake fuskantar wata koma-baya a wannan shekarar. Fushin dabi'ar yanayi. Raguwar ruwan sama da sanyi sun lalata manyan sassan amfanin gona na yankin Sahel na Siriya, kuma samar da amfanin gona da yawa - musamman zaitun - ya ragu. Waɗannan, tare da rashin tallafin gwamnati kamar taki da iri, ƙaruwar farashin sufuri da kuma rushewar saye da siyarwar tsakanin mutane, sun ƙara ta'azzara rikicin.

Wani memba na "Kwamitin Zaman Lafiyar Jama'a" a Tartus ya ce: "Mun yi ƙoƙarin taimakawa wajen samar da damar aiki. Bayan dubban mutane sun rasa tushen samun kuɗin shiga, mun tuntuɓi cibiyoyin gwamnati kuma muka nemi tallafi ga manoma, makiyayan dabbobi da ƙarfafa haɗin gwiwar noma; ƙungiyoyin haɗin gwiwa waɗanda za su iya rage wani ɓangare na nauyin gwamnati da kuma ƙara yawan samar da kayayyaki.

Amma a cewarsa, duk da duk alkawuran, babu abin da aka aiwatar a ƙasa. An tilasta wa mutane su sayar da wani ɓangare na ƙasarsu, su sare bishiyoyin 'ya'yan itace don amfani da itacensu don dumama a lokacin hunturu; kawai don ceton kansu daga yunwa da sarai da fatan wataƙila wata rana yanayin zai canza.

................................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha